Mark 4

1Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun. 2Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu,

3“ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka. 4Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa.

6Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe. 7Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba.

8Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari”. 9Sai ya ce, Duk mai kunnen ji, ya ji,”

10Sa’adda Yesu yake shi kadai, wadanda suke kusa dashi tare da sha biyun suka tambaye shi ma’anar misalan. 11Sai ya ce masu, “ku an yardar maku, ku san asirin mulkin Allah, amma ga wadanda ba su cikinku, komai sai a cikin Misalai, 12don gani da ido sun gani, amma ba su gane ba. ji kuma, sun ji, amma ba su fahimta ba, don kada su juyo a gafarta masu,”

13Ya ce masu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran? 14Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa. 15Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu.

16Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki. 17Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube.

18Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar, 19amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani. 20Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari.”

21ya ce masu, “Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta. 22Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba. 23Bari mai kunnen ji, ya ji!‘’

24Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka. 25Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi.”

26Sai ya ce, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa. 27A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba. 28Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko, 29Sai kai, sa’anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan.”

30Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya. 32Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta.”

33Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu, 34ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu.

35A ranan nan da yama ta yi yace masu “Mu haye wancan ketaren.” 36Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi. 37Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika.

38Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa “Malam za mu hallaka ba ka kula ba?” 39Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun,, “Ka natsu! ka yi shiru!” Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru.

40Ya ce masu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?” Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, “wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?”

41

Copyright information for HauULB